December 7, 2025

Ƴantawayen Syria Sun Ce Sun Ƙwace Birnin Damascus

images-2024-12-08T100143.033.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban kungiyar ‘yan tawayen da ke jagorantar yakin Syria, Abu Mohammed al-Jawlani, ya ce mayakansu sun samu nasarar ƙwace babban birnin ƙasar, Damascus.

Al-Jawlani ya bayyana wannan nasara a matsayin wata babbar tarihi, tare da gargadi ga mayakansa da su guji cutar da duk wanda ya mika wuya.

Tun da farko, ‘yan tawayen sun bayyana cewa sun kama birnin Homs, wanda ke zama birni na uku mafi girma a Syria.

Rahotanni kuma sun nuna cewa ‘yan tawayen sun shiga Damascus, yayin da ake zargin cewa Shugaba Bashar al-Assad ya tsere, ba tare da sanin inda ya ke ba.