Ƴanta’addan da suka kashe Sarkin Gobir sun ce sai an ba su naira miliyan 69 da babura 5 kafin su saki gawarsa
Daga Sabiu Abdullahi
‘Yan ta’addan da suka kashe Sarkin Gobir na gundumar Gatawa a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Muhammad Bawa, sun ce sai biya musu wasu buƙatunsu kafin su sako gawarsa.
Suna neman kudin fansa naira miliyan 60 da babura biyar a madadin gawar, wanda har yanzu suna ci gaba da rikewa.
Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da basaraken gargajiyar, da azabtarwa da kuma kashe shi a ranar Laraba.
Wani faifan bidiyo mai ban tausayi ya bayyana wanda ke nuna Alhaji Bawa yana rokon a ceci rayuwarsa tare da rokon gwamnati ta sa baki.
Tun da farko dai masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su makudan kudade har Naira biliyan daya domin su sako Alhaji Bawa da dansa da aka yi garkuwa da su a watan Yuli.
Wani faifan bidiyo mai ratsa zuciya ya nuna sarkin gargajiya yana ba da labarin abin da ya faru da shi mai ban tsoro kuma yana neman taimako.
Sai dai kuma abin takaici shi ne, da alamu an yi kunnen uwar shegu da rokon da ya yi na a ceto shi.
A yanzu dai iyalansa na fuskantar yiwuwar rashin iya yi masa jana’iza bisa tsarin Musulunci da ta dace idan har suka kasa biyan bukatun ‘yan ta’addan.
Wata majiya ta iyalinsa ta bayyana cewa “Sun ce kafin su saki gawarsa dole ne mu ba su Naira miliyan 60 da babura biyar,” kamar yadda Sahara Reporters ta ambato.




