January 16, 2026

Ƴanta’adda sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a Zamfara

IMG-20240910-WA0013

Daga Sabiu Abdullahi  

Wani mummunan harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai a karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, ya yi sanadin kashe jami’an ‘yan sanda biyar da sojoji uku.  

Jami’an tsaron na rakiyar ma’aikatan kamfanin Setraco Nigeria Limited ne a lokacin da aka kai musu harin da safiyar Alhamis.  

Wata majiyar soji ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa, “Dakarun da ke raka ma’aikatan Setraco a hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Tsafe a Zamfara sun ci karo da wani kwanton bauna.  

Majiyar ta bayyana cewa an kashe sojoji uku da ‘yan sanda biyar, sannan ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da bindigu.  

Sai dai kuma martanin da rundunar ta yi cikin gaggawa ta ceci sauran jami’an tsaro da ke aiki a ginin, sannan an kashe ‘yan ta’adda da dama a wani artabu da aka yi da su.

Sannan wasu ‘yan ta’addan sun tsere da makamai da suka sace.  

Majiyar sojojin ta yi kira da a yi wa tawagarsu addu’a a Zamfara.

1 thought on “Ƴanta’adda sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a Zamfara

Comments are closed.