January 15, 2025

Ƴansandan Legas sun kama manajan otal kan mutuwar wata mata

0
IMG-20241007-WA00141.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos ta kama manajan wani otal a unguwar Dopemu bayan mutuwar wata mace da ake zargin ta ziyarci otal ɗin tare da wani mutum da ba a san ko wane ne ba.

A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ofishin ‘yan sanda na Dopemu ya samu rahoto daga manajan otal ɗin da misalin ƙarfe 10:10 na dare a ranar Jumma’a dangane da lamarin.

Hundeyin ya ce manajan otal ɗin ya bada rahoton cewa mutumin da matar sun shiga otal ɗin da misalin ƙarfe 9:30 na dare, inda suka nemi su yi ɗan gajeren lokaci.

Sai dai manajan ya kasa ɗaukar bayanansu.

“Manajan ya ce bayan sa’a ɗaya, matar ta fito da gudu tana cewa tana jin zafi, sannan ya ba ta ruwan sanyi ta sha,” inji Hundeyin.

“Manajan ya ce matar ba ta samu sauki ba, kuma daga bisani aka kai ta wani asibiti a kan titin Dopemu, inda ta rasu, yayin da mutumin da ya kawo ta ɗin ya tsere.”

Manajan otal ɗin yanzu haka yana tsare don taimakawa wajen bincike.

An ajiye gawar matar a dakin ajiyar gawawwaki na babban asibitin Mainland da ke Yaba domin a yi mata binciken musabbabin mutuwarta.

Hundeyin ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike don gano musabbabin mutuwar, gano ainihin matar, da kuma kama mutumin da ya kawo ta otal ɗin.

Lamarin ya tayar da hankula game da tsaro a otal-otal da muhimmancin ɗaukar bayanai da sanya ido yadda ya kamata

‘Yan sanda na kira ga duk wanda ke da wani bayani da zai iya taimaka wa binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *