Ƴansandan Kano sun cafke masu garkuwa da mutane da dama

Daga Abdullahi I. Adam
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Kano, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kame wani gungu na masu garkuwa da mutane a jihar.
Kamar yadda jami’in ya wallafa a shafinsa na Facebook a safiyar nan, Kiyawa ya tabbatar da cewa “a daren jiya a Kwanar Dangora, mun samu wata babbar nasara. Wasu bata gari (kidnappers) sun shigo Jihar Kano da niyyar yin garkuwa, amma yanzu haka suna hannu.”
Bayanan da ya wallafa ba su ambaci yawan ɓata-garin da kuma irin makaman da aka samu a tattare da su ba.
Daga bisani ya ja kunnen ɓata-garin da cewa su kiyayi jihar ta Kano domin wannan ɗanyen aiki nasu ba zai taɓa samun gurin zama a faɗin jihar ba.