December 7, 2025

Ƴansanda suna neman Dr. Idris Dutsen Tanshi ruwa a jallo

images-135.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa tana neman wani malami a jihar mai suna Idris Abdulaziz ruwa a jallo.

An bayyana hakan ne a wata takarda ta ‘yan sanda da aka raba wa manema labarai a Bauchi ranar Alhamis.

Sanarwar da ‘yan sandan suka fitar ta hannun sashen binciken manyan laifuka na rundunar, ta nuna hoton Abdulaziz da cikakkun bayanai tare da yin alkawarin bayar da tukuici ga duk wanda ya taimaka wajen kama shi.

A cewar sanarwar, an bayyana neman Idris Abdulaziz ne bisa zargin raina kotu.

Da aka tuntubi lauyan Idris Abdulaziz kan lamarin, Ahmad Musa, ya ce sanarwar da ‘yan sandan suka yi ba wani sabon abu ba ne domin gwamnatin jihar na amfani da dukiyar kasa wajen danne muryar ‘yan adawa.

Ya ce, “Wannan ba sabon abu ba ne, Malam Idris Abdulaziz ne kadai ke fadin gaskiya a kan mulkin Gwamnatin jihar na amfani da dukiyar kasa wajen danne shi”

Rahotanni sun ruwaito cewa Musa ya zargi gwamnatin jihar Bauchi da yin amfani da bangaren shari’a na jihar wajen cutar da wanda yake karewa a siyasance.

Idan ba a manta ba dai malamin ya shiga sa-in-sa da gwamnatin Jihar Bauchi karƙashin Sanata Bala Abdulqadir Mohammed tun kafin ya sake cin zaɓe na biyu.