March 28, 2025

Ƴansanda Sun Kama Wani Malami Da Ake Zargi Da Kashe Dalibar Da Suka Haɗu A Facebook

image_editor_output_image1758338957-1739639041110.jpg

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta cafke wani mutum mai suna AbdulRahman Bello, wanda ke ikirarin malamin addini ne, bisa zargin kashe wata daliba domin yin asiri.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar, Lawal Hafsoh Yetunde, daliba ce a shekarar ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara, Ilọrin. An ce ta bace tun ranar 10 ga Fabrairu, 2025 bayan halartar suna.

A cewar majiyoyi, yayin da take cin abinci a wurin taron, ta samu kira a waya ta fice daga wurin, kuma daga nan ba a sake jin ɗuriyarta ba. Ana zargin wanda ake tuhuma ya hadu da ita ne ta shafin Facebook, inda ya samu lambar wayarta sannan ya gayyace ta.

Bayan iyayenta sun lura da ɓacewarta, sai suka kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Oja-Oba a Ilorin. Rundunar ‘yan sanda ta bi sahun kiran ƙarshe da aka yi mata, wanda hakan ya kai ga cafke wanda ake zargi a Offa Garage, duk da cewa gidansa yana Isalekoto.

Wata majiya ta bayyana cewa a farkon bincike, wanda ake zargi ya musanta sanin inda dalibar take. Sai dai bayan da aka gudanar da bincike a gidansa, ya amsa cewa lallai ta zo wajensa, amma ta mutu sakamakon ciwon asma.

A cewar majiyar, “An gano gawarta da aka yanka a cikin wata kwano tare da kayan aikin da aka yi amfani da su wajen aikata laifin. Bincike ya nuna alamu cewa ba shi ne karo na farko da yake aikata irin haka ba.”

Wanda ake zargin ana ce masa ɗan wani fitaccen malami ne daga Isalekoto, wanda ya rasu kwanan nan.

Da take tabbatar da lamarin a ranar Asabar, kakakin rundunar ‘yan sanda, Adetoun Ejire-Adeyemi (SP), ta bayyana shi a matsayin “abin tsoro.”