Ƴansanda sun kama mutumin da yake lalata da ɗiyarsa mai shekara 12
Daga Sabiu Abdullahi
Jami’an rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun sun kama Ibrahim Aliu mai shekara 41 da ake zargin yi wa ‘yarsa mai shekara 12 lalata a unguwar Papa Olosun, Oja Odan, a Karamar Hukumar Yewa ta Arewa.
Matar, wadda sun riga sun rabu da ita, Temitope Egbebi, ce ta kai kara ofishin ‘yan sanda na Oja Odan, inda ta zargi Aliu da yin lalata da ‘yarsu a duk lokacin da ta kawo masa ziyara lokacin hutu.
Egbebi ta gano abun da ke faruwa ne bayan ta kai yarinyar asibitin jihar da ke Ilaro domin jinya bayan ta fara fama da zubar wani ruwa daga al’aurarta.
Mai magana da yawun ‘yan sandan, SP Omolola Odutola, ta ce: “Yana yi mata fyade tun kusan shekaru biyu da suka gabata, duk lokacin da yarinyar ta je yin hutu a wurinsa.”
Aliu ya amsa laifinsa yayin da ake yi masa tambayoyi.
Odutola ta kara da cewa: “A ranar Alhamis, da misalin karfe 2:10 na rana, Temitope Egbebi ta kai rahoton rashin da’a na tsohon mijinta, Ibrahim Aliu. An gano cewa yana lalata da ‘yarsu mai shekara 12.”
Za a tura wanda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi a kotu.