Ƴansanda na bincike kan kisan gillar da aka yi wa tsohon janar a Abuja
Daga Sabiu Abdullahi
Benneth Igweh, Kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aiwatar da binciken kisan da wasu da ake zargi ‘yan fashi suka yi wa wani tsohon Janar a gidansa da ke Abuja.
Maharan sun nausa gidan marigayin – Burgediya Janar Uwem Udokwere mai ritaya – inda suka kashe shi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an hallaka tsohon janar ɗin a gidansa da ke rukunin gidajen Sunshine a unguwar Lokogoma da ke birnin tarayyar, ranar Asabar da tsakar dare.
Har ila yau kwamishinan ‘yan sandan ya jajanta wa iyalan marigayin, tare da alƙawarta farauto waɗanda suka yi aika-aikar domin gurfanar da su a gaban shari’a.
Sanarwar ta kara da cewa, ”Za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da kamo maharan domin gurfanar da su a gaban shari’a domin su girbi abin da suka shuka.”