January 14, 2025

‘Ƴansanda ba su kashe mutane a Kano ba’

0
IMG-20240805-WA0005

Rundunar ‘yansandan kasar nan ta karyata wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan’Adam ta Amnesty International ta fitar da ke cewa an kashe akalla mutane 13 a yayin zanga-zangar da aka gudanar a ranar Alhamis 1 ga watan Agustan nan.

Dangane da alkaluman mutanen da suka mutu, wanda rundunar ta karyata na kungiyar ta ce gaba daya mutanen da su ka rasa rayukan su, a lokacin zanga-zangar bakwai ne, wasu ba ma a sanadin zanga-zangar ba suka mutu.

A sanarwar da kakakin ‘yansandan na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce, a tsawon kwana biyu na zanga-zangar, mutum hudu sun mutu, talatin da hudu kuma suka samu raunuka a jihar Borno a wani hari na ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.

Ya kara da cewa a karamar hukumar Yauri da ke jihar Kebbi kuma wani dan kungiyar sa-kai ta bijilanti ya harbi wani daga cikin masu zanga-zanga da suke satar kayan mutane, inda mutumin ya mutu.

Kakakin ya ce bayan wadannan da ya bayyana mutum bakwai babu wani da ya mutu a lokacin zanga-zangar.

Sai dai an samu yadda wasu ke fashi da makami da barnatawa da satar kayan jama’a da na hukuma da sauransu a lokacin a cewar kakakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *