Ƴanbindiga Sun Yi Awon-gaba Da Sama Da Mutum 50 A Zamfara
By Sabiu Abdullahi
Mazauna ƙauyen Gidan Maidanko da ke ƙaramar hukumar Maradun, jihar Zamfara, sun tsere daga gidajensu bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai, inda suka yi awon gaba da sama da mutum 50.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan, waɗanda suka yi amfani da muggan makamai, sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Asabar.
Wani mazaunin yankin ya faɗa wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun sace mutane tsakanin 50 zuwa 55, mafi yawansu mata da yara ƙanana.
Duk da haka, har zuwa yanzu, babu wani tuntuɓa da aka samu daga masu garkuwar, kuma ba a tabbatar da asarar rayuka ba ko a ɓangaren maharan ko na mazauna garin.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin tsaro ba su yi karin bayani kan lamarin ba.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce yana kan aiki, yayin da Kwamishinan ‘Yan Sanda, Muhammed Shehu Dalijan, bai amsa kiran wayarsa ba.




Amazing..!! We Wait Your New Post..!! Good Luck..!!
Amazing..!! We Wait Your New Post..!! Good Luck..!!