February 10, 2025

Ƴanbindiga sun kai hari wani ƙauye a Kaduna

0
images-2-13.jpeg

Daga Abdullahi I. Adam

A daren da ya gabata, maharan daji ɗauke da muggan makamai sun afka ƙauyen Turawa da ke Gundumar Kakangi ta Karamar Hukumar Giwa a nan Jihar Kaduna inda suka jikkata wasu da dama kuma suka hallaka wani mazaunin garin.

Bayanai sun ambaci cewa maharan sun afka ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:20 na dare inda suka far wa mutanen ƙauyen da harbe-harben bindigogi da ake zargin ƙirar AK47 ne.

Wani mazaunin garin da muka zanta da shi mai suna Malam Yusuf Muhammad ya bayyana cewa a sa’ilin da maharan suka shigo garin, hankalin jama’a ya tashi matuƙa.

Hakan ya tilasta wa mazauna yankin tunkarar maharan da kuma neman ɗauki daga jami’an tsaro.

Bayanai da muka samu daga mazauna yankin sun nuna cewa duk da cewa an sanar da jami’an tsaro cewa maharan sun afkawa ƙauyen, ba a sami wani ɗauki ba har sai bayan da maharan suka gama cin karensu babu babbaka cikin daren.

Bayan faruwar lamarin, mun sami tabbacin cewa maharan sun hallaka wani magidanci mai sana’ar acaɓa ɗan shekara 25 mai suna Nuhu Jafar sanadiyyar harbinsa da aka yi.

Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa maharan sun jikkata mutane da dama inda a yanzu haka wasunsu ke samun kulawar gaggawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika-Zaria.

Cikin waɗanda suka jikkatan akwai wani ɗan kimanin shekaru 26 mai suna Abdulhamid Maharazu, sai Sulaiman Gambo mai shekaru 25 da Tasiu Abubakar wanda ake kira Gwano mai shekaru 30, sai kuma wani dattijo mai kimanin shekaru 50 mai suna Yusuf Wanzam.

A lokacin haɗa wannan rahoto, wani da muka zanta da shi cikin mazauna yankin ya tabbatar mana da cewa ya zuwa yanzu dai babu wani yunƙuri na ɗaukan mataki da aka samu daga mahukunta duk da sun san halin da yankin ke ciki.

Mutumin ya ce sojoji sun kawo ɗauki ne bayan ‘yan ta’addan sun gama ta’adinsu a garin sun koma daji cikin daren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *