April 19, 2025

Ƴanbindiga sun hallaka mutane 5 a Jihar Filato

images (12) (19)

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe mutane biyar a kauyen Mbar da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato a daren Lahadi.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Barista Farmasum Fuddang, da Amb. Duwam Bosco, shugaban kungiyar Bokkos Cultural Development Council Vanguard (BCDCV), ya fitar a babban birnin jihar ranar Litinin.

A cewar kungiyar, “Muna so mu yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyar da ba su ji ba ba su gani ba a garin Mbar ranar 15 ga watan Satumba, bayan rahotannin sirri da aka samu a baya na kwararar ‘yan ta’adda a yankin.”

Sanarwar ta bayyana cewa, an kai wa matasan hari ne a kan hanyarsu ta daga garin Mbar zuwa kauyen Koh a kan hanyar da ta kewaya kauyen Yelwa Nono tsakanin karfe 7 na dare zuwa karfe 7:30 na yammacin ranar.

234 thoughts on “Ƴanbindiga sun hallaka mutane 5 a Jihar Filato

  1. купить диплом зарегистрированный [url=https://prem-diplom77.ru/]купить диплом зарегистрированный[/url] .

  2. продамус промокод скидка [url=https://vip.mybb.rocks/viewtopic.php?id=8484#p22318]продамус промокод скидка[/url] .

Comments are closed.