Ƴan uwan Nabeeha da ƴan bindiga suka mata kasar gilla sun shaƙi iskar ƴanci
Daga Sabiu Abdullahi
Yan bindiga sun sako ‘yan matan nan biyar daga cikin shida da suka garkuwa da su a Bwari da ke babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Hakan ya biyo bayan kashe daya daga cikin ‘yan matan mai suna Nabeeha kimanin mako biyu da suka gabata, wanda ya tayar da hankalin a Najeriya, musamman a kafofin sada zumunta.
Kafar BBC ta rawaito cewa rundunar ‘yan sanda Najeriya ta ce ita ce ta ”kubutar da ‘yan matan a wani samame da jami’anta suka kai dajin kajuru da ke Kaduna da misalin karfe 11:30 na daren Asabar, 20 ga watan Janairu.”
Sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Josephine Adeh ta fitar na cewa tuni aka hada ‘yan matan da iyayensu.