Ƴan Ta’addan ISWAP Sun Yi Kwanton Bauna Wa Sojoji A Borno
Daga Sabiu Abdullahi
Mayakan ISWAP sun kai wa ayarin sojojin Najeriya hari a daren Juma’a a jihar Borno, inda suka kashe jami’ai da dama ciki har da ’yan CJTF, sannan suka yi garkuwa da wani janar, kamar yadda HumAngle ta ruwaito.
Rahoton ya bayyana cewa janar ɗin da aka sace shi ne kwamandan briagde da yake jagorantar dakarun lokacin harin.
HumAngle ta nuna cewa ko da yake an taɓa kashe manyan jami’an soja a wasu hare-hare da suka gabata, sace jami’i mai wannan matsayi abu ne da ba kasafai yake faruwa ba.
Babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro ko rundunar sojin Najeriya kan lamarin.
Adadin waɗanda suka mutu a harin bai fito fili ba tukuna.Binciken da aka tura wa mai magana da yawun rundunar soji, Onyechi Anele, ba a samu amsa ba.
Karin bayani na tafe…




