February 16, 2025

Ƴan ta’adda sun yi wa wani matashi yankan rago

1
image_editor_output_image62747293-1698832913862.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A wani mummunan yanayi da ke nuna yadda lamarin tsaro a Arewacin Najeriya yake ƙara ta’azzara, ƴan ta’adda sun yi wa wani matashi mai suna Mustapha Idris Matazu yankan rago har lahira.

Bayanin da TCR Hausa ta tattara ya nuna cewa al’amarin ya faeu da matashin ne a hanyarsa ta zuwa Matazu daga Katsina.

An kyautata zaton lamarin ya faru ne a juya Talata.

Ya zuwa yanzu dai, TCR Hausa ta bi wasu fostin-fostin na abokanan a kafafen sada zumunta da suka yi game da mutuwar tasa.

Ibrahim Mahuta ya ce: “Innalillahi wainna ilaihi raji’un 😢

“Wannan da kuke ‘Yan ta’adda ne suka masa yankan rago akan hanyarsa ta zuwa MATAZU daga Katsina. Ya subhannahi 😢

“Allah ya kawo mana karshen waɗannan azzaluman alfarmar annabin rahma S.A.W amin.

Ya zuwa yanzu ba mu samu wani bayani daga hukumar ƴan sanda game da al’amarin ba.

1 thought on “Ƴan ta’adda sun yi wa wani matashi yankan rago

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *