January 15, 2025

Ƴan ta’adda sun yi kisar gilla wa masu yankan katako a jihar Borno

1
images-2023-11-28T161940.839.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Da alamu dai har yanzu tsuguno bai ƙars ba game da harkar tsaro a Arewacin Najeriya inda aƙalla masu yankan katako guda 11 ne rahotanni suka bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun fille kawunansu a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno.

Rahotannin sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kusa da Bale, wani kauye mai nisa a karamar hukumar Damboa.

Wasu majiyoyin ƴan banga na yankin sun bayyana cewa an gano gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su a wurin da misalin ƙarfe 5 na yamma.

“Eh, an gano mutane shida daga wurin da lamarin ya faru da yammacin jiya (Litinin) kuma an sassara gabobinsu. An same su ne a cikin jini saboda an sare dukkan sassan jikinsu gunduwa-gunduwa.”

“Mun yi jana’izar su da yammacin yau kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Kodayake mutane biyar sun bace. Ba mu san ko sun tsere ko kuma an sace su ba,” in ji wata majiyar ‘yan banga.

1 thought on “Ƴan ta’adda sun yi kisar gilla wa masu yankan katako a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *