December 7, 2025

Ƴan ta’adda sun yanke wa wasu hannu a Borno

image_editor_output_image1097321046-1705222271555.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Gabashin Najeriya na nuna cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yanke hannun wasu masunta biyu da suka zarge su da yin sata a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.

Zagazola Makama masanin tsaro dake wallafa bayanai akan yankin tafkin Chadi ya ce mutane biyun na daga cikin rukunin masunta da ke gudanar da sana’arsu ta kamun kifi karkashin ikon kungiyar ta ISWAP.

Wasu bayanai sun ce ƴan ta’addar ISWAP su ne suke kula da ayyukan masuntar inda suke karbar haraji daga wurinsu.

Wata majiyar jami’an tsaron sirri ta ce mayaƙan na ISWAP sun kwace kunshin kifi 8 bayan da suka zargi masuntan da ƙin biyan haraji.