January 24, 2025

Ƴan ta’adda sun sake halaka mutane 12 a Borno, sun raunata wasu daban

0
Nigeria_-_Borno.svg_.png

Daga Sabiu Abdullahi

Al’amarin tsaro yana ta ƙara taɓarɓarewa a Arewacin Najeriya yayin da wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne kuma sanye da kakin soji suka kashe mutane 12 tare da yin garkuwa da daya a kauyukan Gatamarwa da Tsiha da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Daso Kenneth, wanda ya tabbatar da harin, ya ce an gano gawarwaki 12.

“Ƴan ta’addar sun yi ta harbe-harbe a kan mutanen da ke cikin ƙauyuka biyun. Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 12, biyu kuma sun samu raunuka,” kamar yadda ya shaida wa ƴan jarida.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda da sauran shugabannin tsaro sun bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike a kan lamarin domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *