Ƴan Shi’a na gudanar da zanga-zanga a Kaduna
Daga Abdullahi I. Adam
A safiyar Juma’an nan, an ga mabiya Shi’a a tituna cikin garin Kaduna suna zanga-zanga.
Masu zanga-zangar na tafiya ne ɗauke da makamai irinsu adduna da takubba da sanduna ba kamar yadda aka saba ganin zanga-zangar lumana ba.
A yayin haɗa wannan rahoto, masu zanga-zangar sun mamaye titin Ahmadu Bello da ke tsakiyar birnin na Kaduna.
Su dai mabiya Shi’a sun sha samun arangama tsakaninsu da hukumomi musamman a garin Zaria inda an sha rasa rayuka saboda irin wannan zanga-zangar da suke gabatarwa.
Ku saurare mu domin samun ƙarin bayani.