Ƴan sanda a Kaduna sun kama mutumin da ya shahara wajen sace-sacen na’urar POS
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar ƴan sanda a Kaduna ta yi nasarar cafke mutumin da ake zargi da satar na’urar POS don damfarar mutane.
Wani wanda kaidin wannan mutumin ya rutsa da shi, Isah Abdullahi Dankane, ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a jiya Alhamis da daddare.
Ɗankade ya ce, “Cikin ikon Allah tare da taimakon al’umma a wannan kafar ta Facebook, tare da gidajen jaridunmu masu albarka mun samu nasarar kama wannan azzalumin barawon POS a jihar Kaduna. Yanzu haka Yana a hannun ƴan sanda a Rigasa Police Division.
“Bayan na yi posting jiya game da damfarar da wannan azzalumin ya yi mana jiya, abun ya yadu sosai alumma sun taimaka muna matuqa wurin posting da sharing.”
Ya ƙara da cewa, “Dazu da safe misalin karfe 12 na rana ina zaune a office sai ga kiran wani bawan Allah ya ce mun ya ga posting din a jaridar Rariya ya dauki number ta kuma wlh ga mutumin nan ya gani a wani gidan abinci ya yi zaune.
“Na ce mishi don Allah ya duba da kyau dai gudun kada a samu matsala ya ce mun wallahi shi ne, na ce to don Allah ya taimaka muna ya je police station kusa da shi ya yi muna reporting, haka aka yi yana zuwa ya hadani da DPO din wurin muka yi waya na fada masa abunda ya faru duk tunaninsu a jihar Kaduna muke nace mishi wlh a Zamfara ne.
“Nan take suka fita da mota suka kamo shi, an yi masa tambayoyi bai musa ko daya ba, kuma ya shaida masu cewa akwai wani maigidansa da ke Zariya shi yake turawa kudin idan ya yi satar POS din, nan take DPO ya sake kirana ya ce zasu sanya shi mota zuwa Zariya daga Kaduna domin a kamo shi. Saboda binciken ya gano zalunci alumma babu adadi.





This is one of my go-to blogs for inspiration Whether it’s fashion, travel, or self-improvement, you cover it all flawlessly