Ƴan sandan Kano sun sha alwashin aiwatar da umarnin kotu da ya hana a dawo da Sanusi
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana kudurinta na tabbatar da hukuncin da wata kotun tarayya ta bayar na haramta mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin Sarkin Kano.
A wata zantawa da manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar ta Bompai a ranar Asabar, kwamishinan ‘yan sanda Usaini Gumel ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandan da ‘yan uwanta za su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, yana mai gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin tayar da hankali ko hargitsa zaman lafiyar jama’a za a hukunta shi.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa umurnin kotun, wanda mai shari’a A.M. Liman na babbar kotun tarayya a daren Alhamis ya bayar, ya hana gwamnatin jihar Kano mayar da Sarki Sanusi II, wanda aka tsige a watan Maris na 2020.
An bayar da wannan umarni ne duk da cewa mai shari’a Liman ba ya kasar, a halin yanzu yana kasar Amurka.
Wani mai rike da sarautar gargajiya, Aminu Babba-Dan’Agundi da Sarkin Dawaki Babba ne suka shigar da karar, inda suka nemi kotu ta sa baki don hana a dawo da Sarki Sanusi II.
Alkawarin da rundunar ‘yan sandan ta dauka na aiwatar da hukuncin kotun na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun tashe-tashen hankula a jihar, inda da yawa ke fargabar barkewar rikici a kan rikicin masarautar.