May 17, 2025

Ƴan sandan Kano sun kama wani matashi da laifin yin ciki tare da kashe ‘yar uwarsa  

image_editor_output_image-709872167-1704358738202.jpg

Daga Sabiu Abdullahi  

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu gagarumar nasara yayin da wani matashi ya kashe ƴar uwarsa bayan ya mata ciki.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa ta shafinsa na Facebook.

A ranar 20 ga Disamba, 2023, ‘yan sanda sun sami rahoto daga Nura Balarabe, yana sanar da su cewa Ukasha Muhammed, mai shekaru 19, ya hada baki da Chidera Ugwu, mai shekaru 24, don yi wa Amina Bala allurai da kwayoyi, wanda ya haifar da mutuwarta.

Wadanda ake zargin sun amsa laifin, kuma bincike ya nuna cewa Chidera Ugwu ya kasance yana yi wa mata masu juna biyu alluran da suka sa suka mutu.

A wani lamarin kuma, rundunar ‘yan sandan Kano ta kama Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Lagwatsani, mai shekaru 18, saboda kisan gilla da ya yi wa Imam Sani Mohammed Shuaibu.