November 10, 2024

Ƴan sanda sun kashe wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

1

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kashe wani fitaccen mai garkuwa da mutane, Nazifi Ibrahim, mai shekaru 22, a kauyen Unguwar Tsamiya, a karamar hukumar Faskari ta jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Aliyu, ya fitar kuma ya bayyana wa manema labarai ranar Asabar a Katsina.

Mista Aliyu ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandan ta kuma samu nasarar ƙwato wasu tarin alburusai yayin samamen.

Ya ce, “A ranar 11 ga Nuwamba, 2023, da misalin karfe 03:30 na safe, bisa ga bayanan da aka samu, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai irin su AK 47, sun mamaye wata gona da ke bayan kauyen Yankara.

“Bayan samun rahoton, DPO Faskari ya tattara tawagar haɗin gwiwa na jami’an ‘yan sanda, ‘yan banga, da jami’an tsaro zuwa wurin.”

A cewarsa, jami’an rundunar haɗin gwiwa suma sun mayar da martani, inda suka tilastawa ‘yan ta’addan yin watsi da shirin nasu, suka gudu cikin daji.

“Lokacin da ‘yan sandan suka je wurin da lamarin ya faru, sun gano gawar wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne da aka kashe, da kuma harsashi 185 da kuma gidan harsashin AK-47 guda 13 da aka ɓoye a cikin buhu.

1 thought on “Ƴan sanda sun kashe wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *