November 8, 2025

Ƴan sanda sun kama wani riƙaƙƙen ɓarawon shanu a Kaduna

images-2023-12-17T184453.631.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargin barayin shanu ne tare da kwato dabbobi 90 a ranar Asabar a Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Kaduna.

A cewar Hassan, “A ranar 16 ga watan Disamba, da misalin karfe 2130 na safe, jami’anmu da ke sintiri a kusa da Kasuwan Dole a cikin garin Millennium, sun yi nasarar cafke wanda ake zargin, wanda ake zargin dan kabilar Kurmin Kaduna ne a karamar hukumar Igabi ta jihar.”

Hassan ya bayyana cewa wanda ake zargin yana da hannu a cikin satar shanu 65 da tumaki 25.

Ya ce bayan bincike da kuma yi masa tambayoyi, wanda ake zargin bai iya bayar da gamsasshen bayani kan dabbobin ba.

“Hakan ya sa ake zarginsa game da sa hannu a ayyukan sata.

“Sakamakon hakan, an mika wanda ake zargin ga hukumar binciken manyan laifuka (CID). don cikakken bincike da himma,” inji Hassan.

1 thought on “Ƴan sanda sun kama wani riƙaƙƙen ɓarawon shanu a Kaduna

Comments are closed.