Ƴan sanda sun kama mutumin da ya yi ƙaryar an yi garkuwa da shi don ya damfari ƴan uwansa a Abuja

Daga Sabiu Abdullahi
Ƴan sanda a babban birnin tarayya sun karyata rahotannin da ake yadawa cewa an sace wani mutumi a yankin River Park a safiyar ranar Asabar, 20 ga watan Janairu.
A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Abuja ta fitar kuma ta wallafa a shafinta na yanar gizo na X, ta bayyana rahotannin a matsayin karya kuma ta ci gaba da cewa “babu wanda aka yi garkuwa da shi a Estate River Park”.
Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar SP Josephine Adeh, ta kuma nuna cewa an kama wani mutum mai suna Nnandi Agu.
A cewar rundunar, an kama Agu ne bayan da ya yi karyar sace shi domin ya damfari dan uwansa da ke zaune a gidan.
Sanarwar ta ce: “Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja tana sane da labarin da ake ta yadawa game da wani mutumi da ake zargin an yi garkuwa da shi a Estate River Park da sanyin safiyar yau, kuma tana so ta bayyana cewa sabanin rahotanni, babu wanda aka yi garkuwa da shi a Estate River Park.