Ƴan sanda sun kama magidancin da ya yi yunƙurin kashe matarsa a Bauchi
Daga Sabiu Abdullahi
Ƴan sanda a Jihar Bauchi sun samu nasarar kama wani dan kasuwa saboda yunkurin hallaka matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinsu ya kara jari a kasuwancinsa.
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar, Ahmed Wakil, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
A cewar Wakil, magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da tabarya wajen dukan matar tasa da nufin kashe ta.
A halin yanzu dai an kai ta asibiti domin samun kulawa ta musamman sakamakon munanan raunukan da mijin ya yi mata.