January 24, 2025

Ƴan sanda sun kama ɓarayin mota a Kano, sun ƙwato motoci 20

0
FB_IMG_1701849922447.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Talata ta sanar da kama wasu mutane 15 da ake zargi tare da sace motoci a sassa daban-daban na jihar.

A cewar ƴan sanda, ta sun samu nasarar ƙwato aƙalla motoci 20.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano.

Ya ce sun samu nasarar ƙwato motocin da aka sace ɗin ne sakamakon jajircewar da rundunar ta yi na kawo karshen duk wasu laifuka da ake aikatawa a jihar.

Kiyawa ya ce, “Mun himmatu sosai wajen yaƙar satar motoci da duk wani nau’in aika-aika a wuraren da muke sa ido.

“A cikin wata daya da ya gabata, rundunar ‘yan sanda ta ci gaba da nuna aniyarta ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin duk mazauna jihar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *