January 14, 2025

Ƴan sanda sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su, sun kama mutane 18 da ake zargi

0
IMG-20231126-WA0026.jpg

Daga Ɗanlami Malanta

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a ranar Lahadi ta ce ta ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su tare da cafke wani mai karbar haraji da wasu 17 a karamar hukumar Logo ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sewuese Anene, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da muya fitar a Makurdi, babban birnin jihar.

A cewar Mista Anene, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kasuwar Mchia a ranar 23 ga watan Nuwamba a karamar hukumar Logo inda suka yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa guda biyu.

Ya ce bayan samun bayanai kan lamarin sace-sacen da kuma sace ‘yan kasuwa da aka yi, ‘yan sanda sun dauki matakin gaggawa inda suka kai samame a harabar Zaki Tule Nyam, mai karbar haraji.

“Wadanda abin ya shafa sun bayyana cewa an yi garkuwa da su, kuma an bai wa iyalansu mako guda su samo naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa domin a sake su kafin zuwan ‘yan sanda.

“Saboda haka, an kama Zaki Nyam da wasu mutane 17 da ake zargi don ci gaba da bincike.

“Abubuwan da aka kwato daga wurinsu sun hada da bindigar ƙirar kasar Denmark guda daya da adduna,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *