Ƴan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe Nabeeha Bayan Ya Yi Garkuwa Da Ita
Daga Abdulrazak Namadi Liman
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wani Bello Mohammed, mai shekaru 28, dan jihar Zamfara, da ya yi garkuwa da matashiyar nan mai suna Nabeeha a Kaduna.
Jami’in ‘yan sanda a Tafa da ke aikin leken asiri sun kai samame a wani otal da ke Tafa a Kaduna, inda suka kama dan bindigar da kudi naira miliyan biyu da dubu dari biyu da hamsin a hannunsa, wanda ake zargin ya samu ne daga kudin fansa da ya karba daga wadanda suka yi garkuwa da su a yankin.
Wanda ake zargin, a lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa yana cikin ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da ‘yan uwan Barista Ariyo a Bwari, FCT, a ranar 2 ga watan Janairu, 2024, tare da kashe wasu da suka yi garkuwa da su, ciki har da Nabeeha, diyar wani lauya a Abuja, a ranar 13 ga watan Janairu, 2024, a sansanin masu garkuwa da mutane, a jihar Kaduna.
A cikin wani yanayi mai ban mamaki, ya bayar da naira miliyan daya kacal don jawo hankalin DPO, wanda ya ki amincewa da tayin, kuma ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata ya mika shi domin gurfanar da shi a gaban kuliya.