Ƴan sanda sun bankaɗo yunƙurin tayar da hankali bayan yanke hukuncin zaɓen gwamna a Kano
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano a ranar Litinin ta sanar da jama’a shirin wasu kungiyoyin magoya bayan jam’iyyar siyasa na haddasa rikici a jihar.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa, kungiyoyin sun shirya fitowa kan titi domin nuna rashin amincewarsu da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamna a jihar.
Sai dai ya ce rundunar ta dauki matakan tsaro da suka dace domin hana tashe-tashen hankula da ka iya haifar da tabarbarewar doka da oda.
“A kan haka ne rundunar ‘yan sandan ta bayar da wannan gargadi ga mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan domin duk wanda ke da niyyar gudanar da wata zanga-zanga ko jerin gwano to ya yi hakan bisa tanadin doka,” in ji Mista Kiyawa.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Usaini Gumel, ya bukaci mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani nau’i na haramtaccen taro, ko zanga-zanga ko jerin gwano da ka iya jawo tashin hankali.
вывод из запоя анонимно ростов вывод из запоя анонимно ростов .
элитные проститутки http://www.drive-models.ru .
Мобильные приложения позволяют легко скачать приложение БК и начать выигрывать на спортивных событиях