Ƴan sanda a Bauchi sun kama matashin da ya kashe yaro bayan ya yi garkuwa da shi
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da samun nasarar cafke wani da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro dan shekara 12 mai suna Christopher Bala a garin Magama Gumau da ke karamar hukumar Toro.
Yarom, wanda aka yi garkuwa da ahi a lokacin da yanje aika, dan wani jami’in dan sanda ne mai suna ASP Bala Yarima mai kula da shiyya ta Gumau, a jihar Bauchi.
A cewar kakakim rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, a cikin wata sanarwar manema labarai a Bauchi ranar Alhamis, “A ranar 21 ga Maris, 2024, da misalin karfe 0800 na safe, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta samu kiran gaggawa game da sace Christopher Bala dan ASP Bala Yerima, daga garin Gumau.”
Ya kara da cewa, “Bayan samun rahoton, jami’an tsaro daga sashen Toro sun yi hanzarin daukar mataki inda suka fara aikin ceto tare da cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kakakin rundunar ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar, wanda ya gano wani matashi mai shekaru 20 da haihuwa mazaunin Magama Gumau, Rabi’u Adamu a matsayin babban wanda ake zargi da aikata laifin, ya bankado wasu bayanai masu ban tsoro na karbar kudi da alaka ta jini tsakanin wanda ake zargin, da wanda aka kashe, da kuma iyalan wadanda abin ya shafa.
Ya bayyana cewa daga karshe Adamu ya amsa laifin yin garkuwa da shi da kuma kisan gillar da aka yi wa yaron, inda ya amince da karbar kudi naira NGN200,000 a matsayin kudin fansa daga mahaifin wanda aka kashe, ASP Yarima.