January 13, 2025

Ƴan Najeriya 400 da aka koro daga Hadaddiyar Daular Larabawa sun iso Abuja  

0
UAE

Daga Sabiu Abdullahi  

An kori ‘yan Najeriya dari hudu da suka hada da mata 90 da maza 310 daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kuma sun isa Najeriya, a cewar wani rahoto da gidan talabijin na Najeriya ya bayar.  

Jami’an ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki ne suka tarbi mutanen a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.  

Wannan korar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Najeriya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya sanyawa ‘yan Najeriya takunkumin shiga kasar kusan shekaru biyu da suka gabata, sakamakon takaddamar da ke tsakaninsu.  

Duk da rahotannin yarjejeniyar dage takunkumin tafiye-tafiye, wannan sabuwar korar na nuna cewa har yanzu ba a iya warware batutuwan da ke tsakanin kasashen biyu ba.  

A baya dai gwamnatin tarayya ta dawo da ‘yan Najeriya 190 daga kasar UAE a watan Yulin 2024.  

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar a watan Yulin 2024 cewa ta dage takunkumin da ta kakaba wa ‘yan Najeriyar nan take, sai dai wannan sabuwar korar ta sanya ayar tambaya kan halin da huldar difulomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *