Ƴan majalisar Amurka za su kaɗa kuri’ar haramta TikTok a ƙasarsu
Daga Sabiu Abdullahi
Majalisar wakilan Amurka za ta kada kuri’a a ranar Laraba kan wani kudirin doka da zai tilasta wa TikTok yanke hulda da mai shi na kasar Sin ko kuma a dakatar da kafar a Amurka.
Dokar ita ce babbar barazana ga manhajar, wacce ta yi fice sosai a duk fadin duniya yayin da ta haifar da fargaba a tsakanin gwamnatoci da jami’an tsaro game da ikon mallakar kasar Sin da yuwuwar yin biyayya ga jam’iyyar kwaminisanci a birnin Beijing.
Wataƙila za a kada kuri’ar da misalin karfe 10:00 na safe (1400 GMT).
Babu tabbas kan makomar kudurin a majalisar dattawa, inda manyan mutane ke adawa da yin irin wannan tsattsauran mataki a kan wata babbar manhaja da ke da masu amfani da ita a Amurka sama da miliyan 170.