March 28, 2025

Ƴan Isra’ila 3 Da Ke Hannun Hamas Sun Shaƙi Iskar Ƴanci Ƙarƙashin Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

21551598_0-429-3738-2105.jpeg

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta miƙa mutanen Isra’ila uku da take tsare da su ga kungiyar agaji ta Red Cross waɗanda suka haɗa da Yair Horn, Sagui Dekel-Chen da Alexander Troufanov.

Motocin kungiyar agaji ta Red Cross sun isa wurin da za a yi musayar fursunonin ne a Khan Younis na Gaza, kamar yadda wani bidiyo ya nuna.

Hamas na shirin mika wa kungiyar agaji ta Red Cross, Yair Horn, Sagui Dekel-Chen da kuma Alexabder Troufanov wadanda Isra’ila ta yi garkuwa da su, bayan kokarin shiga tsakani da Masar da Qatar suka yi, ya taimaka wajen ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Hamas da Isra’ila da ta dakatar da fadan kusan wata guda.

Bangaren kungiyar Hamas da ke ɗauke da makamai ya fara shirye-shiryen yin musayar fursunoni da Isra’ila a karkashin kashi na daya na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu.

A cewar wakilin Anadolu, an girke mambobin ƙungiyar a Khan Younis da ke kudancin Gaza a shirye-shiryen miƙa mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa.

Rikicin Gaza da Isra’ila dai ya ɗau tsawon lokaci ana gwabza shi kafin wasu ƙasashe suka shiga tsakanin don kawo karshensa.