January 14, 2025

Ƴan bindiga sun tashi wasu garuruwa a Katsina

0
Gunmen-1024x576.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Ƴanbindiga a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tilasta wa mutanen wasu garuruwa  yin gudun hijira.

Rahotanni sun nuna ƴan ta’addar sur far wa garin Wurma da ke ƙaramar hukumar Kurfi inda suka bude wuta.

Lamarin dai ya sa mutanen yankin gudun hijira domin tsira da ransu zuwa makwabta.

Mazauna garin nun bayyana cewa a halin babu kowa a cikinsa.

Dakta Nasir Baangida Ma’azu, Kwamishinan tsaron jihar Katsina,  ya ce ƴanbindigar sun matsawa yankin.

Ya ce, “Shiga ta farko sun bi gida-gida, shiga ta biyu kuma suka ƙone sansanin ƴansanda, dalilin da ya sa mutane suka gudo.”

A ranar Juma’a wasu al’ummar yankunann na karamar hukumar Kurfi sun gudanar da zanga-zanga kan kan ƙamarin matsalar tsaron da ke addabarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *