January 15, 2025

Ƴan bindiga sun sake sace sama da mutum 60 a Kaduna

0
IMG-20240309-WA0003.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da ke fitowa daga arewa maso yammacin Najeriya, a wani sabon hari da ƴanbindiga suka kai sun sake sace kimanin mutum 61 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.

Kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa BBC ƴanbindigar sun kai harin ne a garin Buda ranar Litinin da daddare suka buɗa wuta.

Sai dai babu wata sanarwa daga hukumomin jihar da jami’an ƴansanda da ke tabbatar da harin ya zuwa yanzu.

Sai dai mazauna yankin sun ce ƴanbindigar sun yi wa garin zobe ne da misalin karfe 11:30 na dare suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *