Ƴan bindiga sun sake kai hari a Zamfara gami da kashe ɗan sanda
Daga Sabiu Abdullahi
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in ‘yan sanda da ke kula da karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara tare da kona ofishin ‘yan sanda.
Wani dan yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya shaida wa ƴan jarida ta wayar tarho cewa ‘yan bindiga dauke da manyan muggan makamai sun kawo hari garin Zurmi, hedikwatar karamar hukumar Zurmi da misalin karfe 5 na yammacin ranar Lahadi.
Ibrahim ya ce, nan take ‘yan bindigar suka isa garin Zurmi, kai tsaye zuwa ofishin ‘yan sanda.
Daga nan sai suka je inda suka fara harbe-harbe, sannan suka kashe DCO tare da raunata wasu jami’an ‘yan sanda kafin su banka wa ofishin ‘yan sandan wuta.
A cewar Ibrahim, ‘yan bindigar sun kai hari ofishin ‘yan sandan ne biyo bayan kashe mutanen su uku da ‘yan banga suka yi.