January 13, 2025

‘Ƴan bindiga sun sace fiye da mutum 100 a Zamfara’

0
images-2023-11-25T165920.833.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu ‘yan bindiga a ranar Juma’a sun yi garkuwa da mutane sama da 100 waɗanda yawancinsu mata da kananan yara ne a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka hudu da suka hada da Mutumji, Sabongari Mahuta, Kwanar Dutsi da Unguwar Kawo, da ke karkashin karamar hukumar Maru, saboda rashin biyan harajin da aka dora wa al’ummar.

Wasu majiyoyi daga Mutumji sun shaida manema labarai cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 8 na dare bayan sallah, inda suka fara harbe-harbe ba da dadewa ba, lamarin da ya tilastawa mazauna garin yin tserewa domin tsira da rayukansu.

Mazauna yankin sun ce wani jagoran ‘yan bindiga da ke aiki a yankin mai suna Damina, ya sanya wa wadannan al’umma harajin amfanin gona na naira miliyan 110, inda ya ba su wa’adin makonni biyu su biya.

Rahotanni sun nuna cewa an dora harajin N50m a kan Mutumji, N30m kan Kwanar Dutsi, N20m kan Sabongari Mahuta da N10m kan Unguwar Kawo.

Wata majiya daga yankin ta ce al’ummomin sun fara tattara kudaden ne lokacin da ‘yan ta’addan suka mamaye al’ummar a yammacin ranar Juma’a.

Ya zuwa yanzu dai TCR ba ta ji labarin wata sanarwa da hukumomi suka sake ga da mummunan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *