January 15, 2025

Ƴan bindiga sun kashe wani basarake tare da sace matarsa

0
images-108.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ne ba sun kai farmaki kauyen Koro da ke jihar Kwara a ranar Alhamis, inda suka kashe Sarkin Koro, Janar Segun Aremu (mai ritaya), da kuma sace matarsa tare da wasu mutane biyu.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi Allah wadai da harin na rashin tausayi, ya kuma dauki kisan Janar Segun Aremu a matsayin “rashin imani.”

Da yake jajantawa al’ummar da ke cikin alhini, Gwamnan ya sha alwashin hukunta wadanda suka aikata laifin.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar, Gwamna AbdulRazaq ya ce, “Tabbas za mu samu wadanda suka aikata laifin kuma mu tabbatar da cewa wannan shi ne laifinsu na karshe na cin zarafin bil’adama.”

Ya tabbatar da goyon bayansa ga mutanen Koro, yana mai cewa, “Zukatanmu sun karaya, kuma muna tare da su a wannan lokaci da kuma kodayaushe.”

Rundunar ‘yan sandan jihar da ke Ilorin ta tabbatar da faruwar lamarin, inda wata majiya mai tushe ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *