April 18, 2025

Ƴan Bindiga Sun Kashe Aƙalla Mutum 51 a Wani Sabon Hari a Jihar Filato

0
FB_IMG_1744653778232

Daga Sabiu Abdullahi

Aƙalla mutum 51 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai a garin Zike da ke yankin Kwall, a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Harin ya auku ne da daren Litinin, kamar yadda hukumomin jihar suka bayyana.

Mai bai wa Gwamnan Filato shawara kan sha’anin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa manema labarai cewa harin ya faru cikin dare, kuma da safiyar Litinin an gano cewa adadin waɗanda suka mutu “ya zarce 40.”

Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Filato ta ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 51.

“Maharan sun shiga ne suka buɗe wuta ne kan mutane suna barci suka ji ruwan harsasai,” in ji shugaban hukumar, Hon. Sunday Abdu.

“Sun kashe mutane a gidaje da kuma kan titi, yanzu an ƙidaya gawarwaki 51,” in ji shi.

Jihar Filato dai ta jima da irin wadannan tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a tsawon shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *