Ƴan bindiga sun hallaka mutane 3 a ƙauyen Kaduna
Daga Abdullahi I. Adam
Da misalin ƙarfe 9:30 na daren jiya ne mahara haye a kan babura suka afka wa ƙauyen Bataro na ƙaramar Hukumar Giwa inda suka ci karensu ba babbaka, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.
Maharan waɗanda an ƙiyasta cewa sun kusa su hamsin sun afka ƙauyen ne ɗauke da muggan makamai da ake zargi har da bindigogi ƙiran AK-47.
Kamar yadda majiyar TCR Hausa ta tabbatar, maharan sun hallaka mutane 3 tare da jikkata wasu da dama waɗanda aka garzaya da su asibitin Fatika domin ceton rayuwarsu da kuma ba su kulawar gaggawa.
Mutanen da ‘yan bindigar suka hallaka sun haɗa da wani magidanci ɗan shekara 27 mai suna Sa’adu Yusuf tare da wani magidancin shi ma ɗan shekara 27 mai suna Ahmad Musa.
Haka nan kuma, ‘yan bindigar sun kashe wani matashi ɗan shekara 26 mai suna Nuhu Harisu.
Majiyarmu ta ƙara cewa “jami’an tsaro ba su kawo ɗauki ba har sai da ‘yan bindigar suka fice bayan sun gama ta’asarsu a garin.”
Mutanen na Bataro sun tabbatar da cewa har zuwa safiyar yau Talata ba’a tantance adadin mutane da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su ba waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara da dama.




