January 15, 2025

Ƴan bindiga a Zamfara sun kashe wani mutumi saboda ya ƙi aurar musu da ƴarsa

9
images-2023-12-20T044442.080.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum a kauyen Kwalfada da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara saboda ya hana ‘yarsa auren dan fashi.

Wani dan kauyen mai suna Mallam Rabo ya shaida wa manema labarai cewa daya daga cikin ‘yan fashin ya nemi auren daya daga cikin ‘yan matan kauyen amma mahaifinta ya ki amincewa.

Mahaifin, a cewar Rabo, ya yanke shawarar bai wa daya daga cikin mutanen kauyen ‘yarsa a maimakon dan fashin.

Rabo ya ce, “Bayan an daura auren ne sai ‘yan bindigar suka dira a garin inda suka kashe mahaifin yarinyar.

“Sun kuma bukaci mijin yarinyar ya sake ta domin abokin ta’addancinsu ya aure ta.

“Sun kuma yi barazanar kashe mijin idan bai bi umarninsu ba.

“Nan da nan mijin ya saki matar kuma ta sake yin aure da dan fashin, wanda nan ya kai ta daji.”

Rabo ya nuna cewa ‘yan fashin sun dade suna furnatar garin kuma babu wani mataki da hukumomi suka dauka na samar da tsaro ga mutane.

A cewarsa, ‘yan fashin sun taɓa dora wa kauyen harajin naira miliyan 4 makonnin da suka gabata.

9 thoughts on “Ƴan bindiga a Zamfara sun kashe wani mutumi saboda ya ƙi aurar musu da ƴarsa

  1. I really like what you uys tsnd to be up too.
    Such clever work andd coverage! Keepp up thhe excellent works guys I’ve added youu
    gyys too myy oown blogroll.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *