April 19, 2025

Ƴan Bindiga a Katsina Sun Sace Mutum Sama da 50 Bayan Sun Kashe Mutum 6

0
images - 2025-04-07T055701.875

Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua da Dandume a jihar Katsina na cikin halin fargaba, bayan da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai hari a wasu ƙauyukan yankin, inda suka sace mutane fiye da 50 tare da kashe mutum 6.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyukan Layin Garaa da ke Funtua da kuma Mai Kwama a Dandume tun daga ranar Asabar, kuma har zuwa rana ta Lahadi suna ci gaba da barna ba tare da an hana su ba.

BBC ta ruwaito Malam Ya’u Ciɓauna, wani mazaunin Layin Garaa, yana cewa maharan sun iso misalin ƙarfe 10:30 na dare, inda suka tafi da maza da mata da ƙananan yara da matan aure har guda 53.

“Sun kashe mutum biyu a Layin Garaa da kuma mutum hudu a Mai Kwama,” in ji shi. Shi ma maigarin Layin Garaa, Mustapha Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa al’ummar garin suna fama da matsin rayuwa, kuma yanzu harin ƴan bindiga ya ƙara dagula lamarin.

Ya kuma yi korafin cewa gwamnati da jami’an tsaro ba su kawo dauki ba, yana mai cewa “Sojoji da ƴansanda ba su yi wani mataki na kawo ɗauki ba.”

A cewar maigarin, wannan matsalar tsaro ta tilastawa mutane barin muhallansu da ɗan abin da ya rage a hannunsu, domin kare rayukansu.

Sai dai hukumar ƴansanda ta jihar Katsina ta ce tana ci gaba da bincike a kan lamarin, kuma ba za ta fitar da sanarwa ba sai bayan kammala binciken.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da zama babban ƙalubale a jihar Katsina, inda al’ummar ke cigaba da kiran gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *