January 24, 2025

ƘURUNƘUS: Tarayyar Turai ta nuna buƙatarta na samar da kasa mai cin gashin kanta wa Falasɗinawa

0
images-2024-01-22T170736.628.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Jami’ai na Ƙungiyar Tarayyar Turai sun tafka muhawara game da nazarin ƙirƙirar ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, inda suke ganin haka ne kawai mafita wajen don samar da salama a Gabas ta Tsakiya.

An ambato Ministar Harkokin Wajen Faransa Stephane Sejourne tana shaida wa manema labarai a Brussels cewa, “Matsayar Benjamin Netanyahu abin damuwa ce. Akwai buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu mai tabbacin tsaro ga kowa.”


Rahotanni sun nuna cewa Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Katz da takwaransa na Jordan Ayman Safadi ma sun je wajen tattaunawar da aka yi a babban birnin ƙasar Belgium.

Ministocin Tarayyar Turai ɗin sun kuma bayyana damuwarsu a kan yadda Firaiminista Benjamin Netanyahu yake watsi da batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *