Ƙungiyar IZALA ta tara ₦112m daga fatun layya
Daga Abdullahi I. Adam
Bayanan da ƙungiyar IZALA ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa ƙungiyar ta aamu nasaran tara naira miliyan ɗari da sha biyu ( ₦ 112,000,000.00) a wajen tattara fatun layyar da ta gabata a shekarar 2024/1445HKamar yadda mai magana da yawun ƙungiyar, Malam Ibrahim Baba Suleiman ya bayyana a shfin Facebook a jiya.
Mal. Ibrahim ya bayyana cewa:”Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau, shi ne ya sanar da hakan bayan ya karɓi rahoton kwamitin wanda shugaban kwamitin Malam Lamara Azare ya bada a Asabar ɗinnan a garin Dutse na jihar Jigawa.”
Sheikh Bala Lau, a cewar ƙungiyar, “ya yaba wa jama’a da suka yi hoɓɓasa wajen ganin sun miƙa fatun layyansu ga ƙungiyar IZALA, ya kuma sha alwashin ci gaba da ayyukan raya addini kamar yadda aka saba da kuɗaɗen a baya, ta yadda ko da wanda ya bada ya koma ga Allah, zai cigaba da samun lada mai gudana daga Allah SWT.”
Ƙungiyar ta IZALA ta bayyana cewa, an gabatar da rahoton ayyukan kwamitin ne a gaban shugabanni da jiga-jigan malaman ƙungiyar a taron majalisar ƙasa da ƙungiyar ta gabatar a birnin Dutsen na jihar Jigawa.
Alƙaluman da ƙungiyar ta fitar sun kawo jerangiyar yadda jihohi suka fafata wajen aikewa da tallafin na fatu, inda rahoton ƙungiyar ya bayyana cewa jihar Sokoto ce zakara a bana.Ga yadda rahoton na bana ya kasance kamar yadda mai magana da yawun ƙungiyar ya bayyana:1-A Bana jihar Sokoto ita tazo ta farko, inda ta samar da naira miliyan goma sha huɗu da dubu ɗari shida da arba’in da biyar da ɗari bakwai da naira biyar kacal (₦ 14,645,705.002).
Jihar Kaduna ita ta zo ta biyu inda ta tara₦12,109,800.003.