June 14, 2025

Ƙungiyar Ɗalibai a Najeriya  Ta Goyi Bayan Rufe Makarantu a Bauchi Domin Azumin Ramadan

image_editor_output_image1703309603-1741016487216.jpg

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen Arewa Maso Gabas ta bayyana goyon bayanta ga matakin da gwamnatin Jihar Bauchi ta dauka na rufe makarantu domin bai wa dalibai da malamai damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.

A wata sanarwa da mataimakin ko’odinetan kungiyar na shiyyar, Sen. Usman Abubakar Mansur, ya fitar, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen ba da damar mayar da hankali kan ibada a wannan wata mai alfarma.

Har ila yau, ya jinjina wa gwamnatin jihar bisa wannan ƙuduri, yana mai cewa hakan zai rage wahala ga dalibai da iyayensu a lokacin azumi.

Kungiyar ta kuma buƙaci sauran jihohin shiyyar Arewa Maso Gabas da su yi koyi da Bauchi ta hanyar ɗaukar irin wannan mataki domin sauƙaƙa wa al’ummar Musulmi gudanar da ibada a watan Ramadan.

1 thought on “Ƙungiyar Ɗalibai a Najeriya  Ta Goyi Bayan Rufe Makarantu a Bauchi Domin Azumin Ramadan

Comments are closed.