Ƙulle-ƙullen bayan fage a kan dambarwar maganar Gwaman Kano a kan Hisbah
Mohammad Qaddam Sidq Isa (Daddy)
A gameda matsalolin da suke da alaka da kare tarbiyar al’umma musamman da sunan addini, akwai kulle-kullen bayan fage masu sarkakiya da suke faruwa tsakanin hukumomin kasashe irin su Nigeria a bangare daya da kuma gwamnatocin kasashen duniya masu karfin fada-aji, a daya bangaren.
Ba wai a Nigeria ba kawai, duk wasu shugabanni a duniya wadanda suke da kishin kare tarbiyar al’umma akan matakai na addini, musamman muslunci, suna fuskantar matsananicin kalu-bale da matsin lamba har ma da barazanar yimusu zagon kasa akan muradunsu na siyasa da sauran muradunsu na duniya.
Matakan yin haka suna farawa ne tun daga matakin kungiyoyin NGO da sauran daidaikun wadanda suke ganin kansu wayayyu masu sassaukan ra’ayi wadanda kuma suke kiran kansu da sunan masu kare hakkin dan adam, ko hakkin mata, ko hakkin yin abinda mutum yaga dama mutukar bai sabawa rubutattun dokokin da akayi yisu a mahangar kasashen yammacin duniya ba, wacce ita kuma mahanga ce bamagujiya wacce bata yadda da wani addini ba.
Ko da yake irin wannan mahanga tafi damuwa da addinin musulunci kasancewarsa addini daya tilo da yakeda cikakken tsarin gina da kuma kare tarbiyar al’umma da kuma daidaikun mutane.
To irin wadanan kungiyoyi da daidaikun ‘wayayyu’ wadanda suke samun tallafi na kudade daga manyan kungoyoyin duniya masu irin wannan manufar, da kuma wadanda suke fatan fara samun irin wannan tallafi daga wadancan manyan kungiyoyin duniya, sune suke rubuta rahotanni na koke daban-daban kuma akai-akai zuwa ga wadancan manyan kungiyoyin duniyar inda suke nuna kukan su akan yadda hukumomi a kasashensu wai suke dakile wa al’umma abinda suke kira wai hakin walwala ta hanyar amfani da dokokin da akayi yisu ta mahangar addini.
Su kuma irin wadancan kungiyoyi na duniya wadanda suke samun cikakken goyon bayan manyan kasashen duniya musamman na turai da Amurka, suna amfani da irin karfin fada-aji da suke dashi akan gwamnatocin wadannan kasashen domin su dauki matakan matsin lamba akan gwamnatocin kasashen da ake rubuta rahotannin koken akansu.
Amma fa abun lura shine, su kansu irin wadannan manyan kungiyoyi na duniya sunfi samun tagomashi da karfafawa daga kasashen Turai din da Amurka karkashin shugabancin jam’iyyun da bamasu ra’ayin ‘yan mazan jiya ba ne. Shi yasa zakaga karfin irin wadannan kungiyoyi yafi bayyana a duniya a duk lokacin da Jam’iyyar Democratic Party take mulki a Amurka ko makamanciyarta ta Labour Party a Birtaniya, balle kuma ace an samu dacewar Shugancin Democrat a Washington da Labour Party a London a lokaci guda.
Kuma ha6akar ayyukan irin wadancan kungiyoyi masu yaki da manufofin tarbiyyar addini ya samu ho66asa ta musamman a duniya tun daga hawan Barack Obama daga Jam’iyyar Democrat shugabancin Amurka a 2009, wanda shi Barack Obama hatta a cikin Democrats din yana shugabantar wani bangare ne da suka fi tsatstsawran ra’ayin yaki da tarbiyar addini acikin al’ummah. Kuma cikin tsawon shugabancinsa na shekara 8 ya taka rawa sosai wajen karfafar kungiyoyin yada fandarewa halayen mazan jiya da addini irinsu kungoyoyin yada liwadi da madugo da abinda ake cewa feminism wadanda suka samu karfin da yanzu ankai matsayin da ‘yan siysasa a kasashen duniya har ruge-ruge sukeyi akan nuna goyon baya garesu, kuma kowa tsoro yakeji ayi masa yarfen cewa baya goyon bayansu.
Ko da yake zuwan Donald Trump daga jam’iyyar Republicans masu ra’ayin ‘yan mazan jiya shugabancin Amurka a shekarar 2017 zuwa 2021, wanda kuma kasancewarsa yana daga cikin na gaba-gaba wajen rashin amincewa da irin wadancan abubuwa, ya taka rawa wajen dan rage karsashin yaduwar wadannan abubuwa a Amurka da duniya baki daya.
Sai dai kuma dawowar ‘yan Democrats karkashin shugabanci Joe Biden tunda daga 2021 har zuwa yanzu, wanda kuma daman shine mataimakin Obama, ya farfado dasu sosai yana kuma ci gaba da taka rawa wajen fantsamar ire-irensu da irin ayyukansu a duniya.
Kasashe irin su Nigeria wadanda kusan babu wani bangaren rayuwa kamar tattalin arziki da siyasa da diflomasiyya wanda suke tsaye akan kafafuwansu akai, sunfi tasirantuwa da matsin lambar da suke samu daga kasashen Turai da Amurka akan irin rahotannin koken da kungiyoyin NGO suke rubutawa manyan kungiyoyi iyeyen gidansu na duniya, wadanda su kuma suke tunzura gwamnatocinsu su aiwatar da matsin lambar.
A cikin satin daya gabata, Malam Aminu Daurawa yayi wani bayani da na ganshi a social media, yana dan karin haske akan irin matsin lambar da suke fuskanta ta hanyar kai kararsu da akeyi zuwa wajen manyan kasashen duniya da Amnesty International da majalisar dinkin duniya a kan cewa wai Hisbah suna wulakanta mata.
Haka abun yake a matakan shugabanci ma. Kai, karewa ma, a kasa kamar Nigeria wacce batada wani katabus agaban kasashen yamma, jakadun kasashe kamar Amurka da Birtaniya da Faransa a Abuja su kadai sun isa su aiwatar da matsin lambar kasashensu akan shugabannin Nigeria don ayi abinda sukeso ayi ko kar ayi abinda basaso.
A irin wannan dambarwar da takaiga Mallam Aminu Daurawa ya ajye aikin shigabancin Hisbah a Kano, irin bayanan da gwamna Abba yayi akan Hisbah basu wuce sakamakon irin wancan matsin lambar bane kai tsaye daga cibiyoyi da kuma gwamnatocin kasashen yamma, da kuma matsin lamba daga ita kanta gwamnatin Nigeria wacce ita ma take fuskantar irin matsin lambar daga wajen kasashen yamman.
Tabbas saboda dalilai na siyasa da tasirin da matakin Mallam Daurawa zai iya yi akan siyasar Gwamna Abba, ba mamaki Gwamna ya nemi sasantawa da Mallam akan ya jingine matakinsa na ajiye aikin shugabancin Hisbah, amma ko anci nasarar shawo kan Mallam ko ba’aiba, wadannan kulle-kullen bayan fagen zasuci gaba da faruwa, kuma kullun zasuci gaba da nuna gaskiya ko rashin gaskiyar gwamnan da yake kan mulki gameda abinda ya shafi ayyukan Hisbah.