Ƙasashe Burkina Faso Da Mali Da Nijar Sun Fice Daga ECOWAS

Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatocin soji a kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar da ficewa daga kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka cikin gaggawa.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya rawaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin kasashen Sahel uku suka fitar da wata sanarwa suna masu cewa “hukunci ne mai girma” na ficewa daga kungiyar ECOWAS ba tare da bata lokaci ba.
An dakatar da dukkan ƙasashen uku daga kungiyar ECOWAS, inda Nijar da Mali ke fuskantar matsanancin takunkumi.
Firaministan da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta nada a ranar Alhamis ya caccaki kungiyar ECOWAS bayan da kungiyar ta yi watsi da taron da aka shirya yi a birnin Yamai na Nijar
Мобильные ставки доступны каждому — просто скачайте приложение БК и начните выигрывать